Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane 65 A New Zealand


Mutane suke taimakawa wadanda suka jikkata a girgizar kasar da ta aukawa New Zealand Talatan nan.

Frayin Ministan New Zealand ya ce akalla mutane 65 ne girgizar kasar da ta aukawa birnin ChristChurch,ta rusa gine gine cike da mutane suna bakin aiki.

Frayin Ministan New Zealand ya ce akalla mutane 65 ne girgizar kasar da ta aukawa birnin ChristChurch,ta rusa gine gine cike da mutane suna bakin aiki.

Frayin Minista John Key yace girgizar mai karfin awo 6.3 ta auku ne da tsakar ranar yau talata agogon kasar. Ya kira girgi-zar, mummunar bala’I da ta afkawa jama’ar birnin.

‘Yansanda sun bada labarin hasarar rayuka da kuma gine gine da dama sun sami lahani cikin birnin. A wasu sassan birnin layukan wutan lantarki da na tarho sun katse.

Gidan Radiyon NewZealand ya bada labarin dubban mutane sun gudu sun taru kan titunan birnin.Wani coci da bashi da nisa da tashar radiyon ya fadi,wata gada kuma ta lalace.

XS
SM
MD
LG