Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar juyin juyin halin na ci gaba da kadawa a kasashe da dama


Iranian regime loyalists hold a poster with doctored pictures of former president Mohammad Khatami (L) and opposition leaders Mir Hossein Mousavi (C) and Mehdi Karroubi on the gallows during a pro-government demonstration in Tehran, February 18, 2011

Guguwar juyin juyin halin na ci gaba da kadawa a kasashe da dama, domin kuwa an ci gaba da yin zanga zangar kin jinin gwamnati a jiya juma’a a kasashe da dama a gabas ta tsakiya da arewacin Afrika a yayinda dubban mutane suka yi gangamin neman canji.

Guguwar juyin juyin halin na ci gaba da kadawa a kasashe da dama, domin kuwa an ci gaba da yin zanga zangar kin jinin gwamnati a jiya juma’a a kasashe da dama a gabas ta tsakiya da arewacin Afrika a yayinda dubban mutane suka yi gangamin neman canji. A kasar Baharain sai da jami’an tsaro suka yi harbi a yayinda masu zaman makoki da suke barin wurin jana’iza suka yi kokarin komawa dandalin dake tsakiyar baban birnin kasar, domin bijirewa haramta yin zanga zangar. Shedun gani da ido sunce mutane da dama ne suka ji rauni a sumamen da jami’an tsaro suka kai. Baban shugaban yan darikar Shiya na kasar ya baiyana sumamen da yan sanda suka kaiwa masu zanga zangar a zaman kisan kiyashi. A kasar Yamal kuma, an kashe akalla mutum guda, mutane ashirin da takwasu kuma suka ji rauni a lokacinda wani mutum dake cikin wata mota ya jefi taron masu zanga zangar kin jinin gwamnati da nakiya a birnin Taiz dake kusu maso yammacin kasar. An kai harin ne a yayinda masu zanga zangar da suka kira gangamin ranar nuna bacin rai da aka yi a duk fadin kasar. Wasu shedun gani da ido sun dorawa gwamnati alhakin harin. A kasar Jordan kuwa zanga zangar ce ta buge da zama tarzoma a yayinda magoya bayan gwamnati suka yi arangamar da masu zanga zangar dake bukatar a gudanar da sauye sauyen harkokin siyasa. An bada rahoton cewa akalla mutane takwas aka jiwa rauni a lokacinda magoya bayan gwamnati suka kaiwa masu zanga zangar hari da kulake. A can kasar Iran ma bata canja zani ba, domin dubban magoya bayan gwamnati ne suka bukaci a kashe shugabanin masu hamaiya Mir Hossein Mousavi da Mehdi Karaoubi a lokacin salar juma’a a birnin Tehran. Anyi wannan kiran ne kafin ayi zanga zangar kin jinin gwamnati da aka bukaci ayi a jiya juma’a. A can kasar Masar kuwa rundunar soja tace ba zata bari ayi zanga zangar da yajin aikin da suke kasara tattalin arzikin kasar ba. Dubban mutane ne suka taro a dandalin Tahrir domin bikin cika mako guda tun lokacinda shugaba Hosni Mubarak ya ajiye ragamar mulki. Magoya bayan mulkin democradiya suna ta daga tutar Masar a lokacin da aka yi bukukuwan da suka hada harda wake wae da raye raye. A Libya kuwa kungiyar hankoron kare hakkin jama’a ta Human Rights Watch tace jami’an tsaro sun kashe masu zanga zangar ashirin da hudu a lokacinda suka kaiwa masu zanga zangar kin jinin gwamnati sumame. Kungiyar Human rights Watch ta ambaci shedun gani da ido na fadin cewa jami’an tsaro ne suka harbe masu zanga zangar a wani yunkurin tarwatsa zanga zangar da aka yi a duk fadin kasar.

XS
SM
MD
LG