Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tun Litinin Gobara Take Ci a Wani Bene Mai Hawa 24 a Legas


Wani dan kwana kwana yake kokarin kashe wata wutar daji anan Amurka.
Wani dan kwana kwana yake kokarin kashe wata wutar daji anan Amurka.

Har yanzu wani bene mai hawa 24 yana ci da wuta a tsakiyar birnin Legas tun safiyar litinin.

Zuwa yanzu dai hukumomi a jihar Legas basu bayyana musabbabin gobarar da har yanzu take ci a wani bene mai hawa 24 inda kamfanoni da 'yan kasuwa suke da shaguna ba.

Har zuwa lokacinda muke gabatar muku da wannan labarai, ‘yan kwana kwana suna kai goro su kai mari a kokarinsu na shawo kan gobarar, amma babu alamar suna samun galaba.

Wakilinmu a legas Ladan Ibrahim Ayawa, yace gobarar wacce ta faro daga hawa na daya yanzu ta kai hawa na biyar.

Wannan babban ginin yana kunshe da kamfanoni da ‘yan kasuwa daban daban na cikin gida da wajen Najeriya. Ladan yace akwai ma Banki a cikin wanan gini.

Zuwa yanzu dai bamu sami labarin hasarar rayuka ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG