Accessibility links

Biyar Daga Cikin Gwamnonin PDP7, Sun Ziyarci Obasanjo

  • Aliyu Imam

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obsanjo.

Gwamnoni biyar cikin bakwai masu adawa da jam'iyyarsu ta PDP sun kaiwa tsohon shugaban kasa Obsanjo ziyara.

Abeoukuta-Gwamnoni biyar daga cikin bakwai masu jayayya da uwar jam'iyyarsu ta PDP mai mulkin Najeriya, sun kaiwa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obsanjo ziyara, a gidansa dake birnin Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Wakilinmu dake yankin, Hassan Umaru Tambuwal ya ce, shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Niger Dr. Mu’azu Babangida Aliyu, ya jagoranci wasu takwarorinsa gwamnoni hudu, suka kaiwa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obsanjo ziyara, a gidansa dake birnin Abekuta fadar jihar Ogun.

Da yake magana da manema labarai gwamna Mu’azu yace suna fatan nan bada jumawa ba za’a kawo ga karshen rikicin da ake fama da shi cikin jam’iyyar ta PDP. Gwamnan Mu’azu yace idan za’a iya tunawa lokacinda aka fara rikicin cikin jam’iyyar su gwamnonin suka fara tuntubar dattijai kan al’amura da suka shafi kasa baki daya. Wannan ziyara ci gaba ne da tuntubar da suka fara.

Gwamna Mu’azu Babangida ya kara da cewa bayan lafawar tuntubar da suka yi, sun ga akwai bukatar a ci gaba da haka domin ganin ko akwai wani canji da aka samu, kuma suna farin cikin bayyana cewa kome yana tafiya kamar yadda ya kamata.

Gwamnonin da suke cikin ayarin har da Sule Lamido na jihar Jigawa, da Rabi’u Musa Kwankwaso na jihar Kano, da Murtala Nyako na jihar Adamawa, da Rotimi Ameachi na jihar Rivers. Saura biyu da basu sami zuwa ba sun hada da Abdulfatai Ahmed na jihar kwara da kuma Aliyu Magatakarda Wamako na jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG