Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Mutane 20 A Koriya Ta Kudu

Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu, bayan da wata gobara ta tashi a wasu gidaje da ke dauke da wani wurin motsa jiki a Birnin Jecheon da ke kasar Korea ta Kudu.

Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu, bayan da wata gobara ta tashi a wasu gidaje da ke dauke da wani wurin motsa jiki a Birnin Jecheon da ke kasar Korea ta Kudu.
Hukumar kashe gobara a kasar ta ce mafi aksarin wadanda suka mutu, suna cikin wurin wankan gasa jiki ne da ake kira Sauna a turance.
Wutar kuma ta faro ne daga wata mota sannan ta mamaye ginin mai benaye takwas, inda mutane da dama suka makale.
Wani Kakakin hukumar kashe gobarar ya ce wutar ta haifar da hayaki mai cike da guba, lamarin da ya sa aka kasa kwashe mutane da dama.
Shi dai Birnin Jecheon, yana dauke ne da tsaunuka da koguna da ke kwarara, yana kuma da tazarar tafiyar kilomita 118 daga Seoul, babban Birnin kasar ta Korea ta Kudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG