Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Mutane A Kalla 70 a Bangladesh


A wani al'amari mai tayar da hankali, wata babbar gobara ta kashe mutane da dama a Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh baya ga mummunar barna da ta yi.

Wata babbar gobara, wadda ta yi kaca-kaca da rukunin gidajen haya a Dhaka babban birniin kasar Bangladesh, ta hallaka mutane akalla 70 a wani sashi mai cike da tarihi.

Gobarar ta tashi ne da daren jiya Laraba a daya daga cikin rukunin gidajen da ke shiyyar Chawkbazar na birnin na Dhaka, kafin ta wanzu cikin lokaci kankani zuwa akalla wasu gine-ginen kuma guda huda.

‘Yan kwana-kwana sun ce akasarin wadanda abin ya rutsa da su sun makale ne cikin gidajen. Akalla wasu mutanen kuma 50 sun ji raunuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG