Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara: 'Yan Kwana-kwana Suna Aiki Tukuru Domin Ceto Mazauna Wani Bene Mai Hawa 27 A London


Hayaki data turnuke wani bene a yammacin birnin London.

Jami’ai sun nuna baiyana fargaban cewa har yanzu kwai wasu mazauna gidan da suka makale a cikin wutar.

Ma’aikatan ceto a birnin London suna aiki gadan gadan don ceto mazuna wani bene mai hawa 27 da gobara mai karfi ta tashi a ciki data yi sa’o’i da dama tana ci. Jami’ai sun nuna baiyana fargaban cewa har yanzu kwai wasu mazauna gidan da suka makale a cikin wutar. Mutane da dama ne suka bace, har da kananan yara.

Magajin birnin London Sadiq Khan ya ayyana gobarar babban hatsari.
Jami’an yan sandan birnin London sun ce akalla ma’aikatar kashe gobara dari biyu ne kokarin kashe wutar, yayin da suke fitar da mutane daga cikin ginin.

Ma’aikatar ceton suna jinyar mutanen da suka shaki hayaki da kuma wadanda suka ji raunuka.

Wasu da suka shedi lamarin sun fadawa wani gidan telbijin birnin cewar suna jin ihun mutane a cikin gida suna neman a taimaka musu, yayin da wasu kuma suka kunnan fitilun wayoyinsu don masu ceton su gano inda suke a cikin gidan.

Ya zuwa wannan safiya ginin bene na ci gaba da konewa.

Tin Downe wani makwapcin ginin ya fadawa Sky News cewa mawuyacin abu ne a samu wani abin da ya rage a cikin ginin.Wadanda suka kubuta sun fito suna tsaye da rigunan bacci yayin da yan sanda suka likace wurin suna kira ga mutane da kada su doshi titunan da suke kusa, domin motocin ayyukan gaggawa su samu sukunin shigewa. An fara bada labarin gobarar ce da karfe daya na dare agogon London.

Masu bincike sun ce ya zuwa yanzu basu san mafarin gobarar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG