Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobarar Notre Dame: UNESCO Ta Kai Ziyara Faransa


Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a lokacin da yake wa Faransawa jawabi kan gobarar Notre Dame ta talbijin
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a lokacin da yake wa Faransawa jawabi kan gobarar Notre Dame ta talbijin

Shugaba Macron ya sha alwashin kammala sake gina Cocin nan da shekarar 2024, inda ake sa ran za ta kasance a kammale, nan da lokacin da kasar ta Faransa za ta karbi bakuncin gasar wasannin Olympics da za a yi a lokacin bazara.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya gana da wata tawagar hukumar ilimi da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, bayan ibtila’in gobara da ya abkawa Mujami’ar Notre Dame.

A jiya Juma’a Macron ya hadu da tawagar a fadarsa ta Elysee.

Tun a shekarar 1991, hukumar ta UNESCO ta saka Mujami’ar ta Notre Dame a jerin wuraren tarihi na duniya, wacce a yanzu bayanai ke nuni da cewa kashi biyu cikin ukun Cocin duk ya lalace sanadiyyar gobarar.

Shugaba Macron ya sha alwashin kammala sake gina Cocin nan da shekarar 2024, inda ake sa ran za ta kasance a kammale, nan da lokacin da kasar ta Faransa za ta karbi bakuncin wasannin Olympics da za a yi a lokacin bazara.

Wasu kwararru dai sun ce, kammala aikin Muja’mi’ar zuwa wannan lokaci, abu ne mai wuyar gani.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG