Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Alhamis a Birtaniya Za a Gudanar Da Babban Zabe


Biyo bayan jerin hare-haren ta’addanci da aka kai cikin wannan makon, Birtaniya zata gudanar da babban zabenta ranar Alhamis, kuma batun matakan tsaro ya zamanto kan gaba.

Cikin jimamin hare-haren Fara Ministar Birtaniya Theresa May, ta ce tura ta kai bango, ya isa haka nan! Kuma tayi gargadin cewa Birtaniya na bukatar sauyi sosai ga yadda take tunkarar lamarin.

A halin yanzu kuma, babban birnin Birtaniya na ci gaba kan tafarkin matakan da aka ‘dauka dalilin sabuwar barazana. An girke ‘yan Sanda ‘dauke da makamai a wasu guraren da mutane suke hada-hada irin su tashar jiragen ‘kasa da guraren da masu yawan bude ido ke kai ziyara.

Amma bayan wannan matakai da aka ‘dauka, ta ya Birtaniya za ta kare kanta? Wannan itace tambayar da ke akan gaba a kasar, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe.

Da take kamfen a jiya Talata, Fara Minista Theresa May ta yi alkawarin samarwa da jami’an tsaro kayan aikin da suke bukata wajen gudanar da ayyukansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG