Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe majalisar dokokin Afirka ta Kudu zata fara muhawara akan tsige shugaba Zuma


Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma

Ranar Talata Majalisar Dokokin kasar Afirka ta Kudu zata bude muhawarar kan neman tsige shugaban kasar Jocub Zuma da ‘yan jami’yyar adawa suka gabatar musu game da cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

A makon da ya gabata ne dai kotu ta yi hukuncin cewa dole sai Mista Zuma ya maida kudaden al’ummar kasa da ya diba yayi amfani da su wajen gyara gidan sa na kashin kansa.

Kudin da aka yi amfani da su sun haura Dalar Amurka Miliyan 20, wajen gyaran gidan nasa da ya hada da gina sabon gulbin wanka da wajen kallon majigi da kuma kewaye inda za ajiye shanun gidan gona. Hukumar yaki da almundahana da dukiyar kasa, ta umarci Zuma da ya biya kudin da yayi bukatar kansa da su ba tare da wani abu da ya shafi tsaron kasa ba.

Zuma yayi bayani da kansa a jawabin da aka yada a talbijin. Zuma yace, “ba tare da saninsa ko da gangan ne ya sabawa kundin tsarin mulkin ba, wanda shine babban kundin dokar kasar”. An dai taba irin wannan yunkuri da zaben tsige shin ya sha kasa.

XS
SM
MD
LG