Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gocewar Laka A Uganda Ta Halaka Akalla Mutane 18


Antony Odiya, manomi ne dake fuskantar matsalar amfani da gonar su ta gado yake noman dankali a dan filin nan.
Antony Odiya, manomi ne dake fuskantar matsalar amfani da gonar su ta gado yake noman dankali a dan filin nan.

Jami’an ayyukan ceto a kasar Uganda sun dakatar da binciken ko akwai mutanen da suka rayu daga matsalar Zamiya da tsagewar da kasa ta rika yi tana haifar da ramuka masu zurfi mutane na fadawa.

Jami’an ayyukan ceto a kasar Uganda sun dakatar da binciken ko akwai mutanen da suka rayu daga matsalar Zamiya da tsagewar da kasa ta rika yi tana haifar da ramuka masu zurfi mutane na fadawa.An kiyasta zamiyar kasar ta kashe mutane akalla goma sha takwas, a yankin gabashin tsaunukan Elgon.

Anji Ministan ayyaukan agajin gaggawa na kasar Uganda na cewa duk da cewa akwai sauran mutane da ake tsammanin suna binne a karkashin kasar amma an fidda tsammanin za’a samesu a raye.

Minista Stephen Malinga yace maimakon binciken ko akwai wadanda suka rayu, yanzu jami’an sun koma ga tattara gawarwakin wadanda suka rasu domin zuwa binnewa.

Mutane sama da metan suka rasa muhallinsu a lardin Bududa. Ruwan sama da aka rika tafkawa mai karfin gaske kuma mai yawa ne ya haifar da matsalar tsagewar da haifar da zamiyar kasa a yankin tsaunukan gabashin Elgon-kasar Uganda jiya litinin.

XS
SM
MD
LG