Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GOMBE: An Kafa Dokar Bahaya Da Kama Ruwa A Fili


Hukumomi a jihar Gombe shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya sun haramta yin bahaya da kuma kama ruwa akan hanya dakuma filaye domin tabbatar da ganin wannan haramci ya kankama, gwamnatin jihar ta samar da kotun tafi da gidanka ta muasamman domin hukunci dangane da wannan dabi’ar.

Kwamishiniyar kula da muhalli ta jihar Gombe, Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha, ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa bahaya da kama ruwa da jama’a ke yi a fili na haifar da matsalar gurbata muhalli, ta kuma yi bayanin yadda za a magance matsalar da kuma yadda za’a hukunta duk wanda ya taka dokar.

Jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan dalilan dake sa jama’a kama ruwa ko yin bahaya a duk inda suka sami dama, lamarin da yawanci suka jingina a kan talauci, domin a cewarsu, da farko akwai ma’aikatan duba gari wadanda ke kula da tsabatace muhaalli.

Alhaji Babayo Aliyu Suleman, ko’odinatan kungiyar Jewel Habitant 2000 and beyond, dake yaki da gurbatar muhalli da dumamar yanayi ya ce samar da wuraren sauke larura zai takaita bazuwar cututtuka da kuma karin lafaiya ga al’ummar jihar.

A daya bangaren kuma, wannan zai samawa jama’a da dama hanyoyin samun kudade kamar yadda ake yi a da, mutane kan gina gidajen bahaya wanda jama’a ke biya domin su sauke larura.

Ga Abdulwahab Muhammed da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG