Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GOMBE: Wasu da Takardun Jefa Kuri'u Sun Shiga Wata Makaranta


Akwatunan zabe

Rundunar 'yansandan jihar Gombe tana binciken gano wadanda suka shiga wata makaranta suna neman dalibai su dangwala masu hannu a kan takardun kuri'un zabe.

DSP Faji Attajiri kakakin rundunar 'yansandan jihar Gombe shi ya yiwa Muryar Amurka karin haske akan lamarin.

Yace wadanda suka gansu sun fara bada shaida. Ya kara da cewa duk wadanda zasu tada zaune tsaye a jihar zasu ji masu.Rundunar ta yI gargadin cewa duk wanda ya yi kokarin tada hankali zasu hukuntashi.

Shugaban makarantar sakandaren a Gombe ya yi bayani. Ahmed Madugu yace da misalin karfe goma sha biyu wasu zauna gari banza suka tsallako katangar makarantar suka shiga.Suka nufi gidajen kwanan dalibai.

Mutanen su shida ne dauke da katin shaida na PDP. Sun kira wasu daliban suka ce zasu daukesu hoton bidiyo. Daliban suka fada masu cewa sai sun gayawa shugabannin makarantar kafin su dauki hotonsu. Sun kuma yiwa daliban alkawarin basu nagoro bayan daukan hotin bidiyon. A lokacin ne daya daga cikin daliban ya gudu zuwa wurin mataimakin shugaban makarantar ya shaida masa abun dake faruwa.

Daga nan aka fadawa jami'an tsaro amma kafin su kai wurin mutanen shida sun arce da gudu sun sake tsallake katangar makarantar.

Daya daga cikin daliban da suka ga mutanen yace sun nemi dalibai su tayasu dangwala hannu a kuri'u da alkawarin cewa zasu basu wani abu..Sun fada ma daliban cewa duk wanda ya dangwala masu hannu zasu dauki hotonsa kuma zasu bashi kudi.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG