WASHINGTON, DC —
A kashi na biyu na bayani kan batun cin zarafin wani karamin yaro kurma dan shekara shida a makarantar kurame ta gwamnati dake Kuje, Abuja, mahaifiyar yaron, Dr Hannatu Ayuba Usman ta bayyana irin matakan da suka bi na neman karin haske game da lamarin daga hukumar makarantar, da kuma yadda suka gamu da cikas.
Saurari bayanin nata
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.