A ciba da yin dubi kan batun ba mata kashi talatin da biyar cikin dari na mukaman siyasa na dori ba zabe ba, yau bakin namu, Hajiya Hauwa El-yakub wadda ta tsaya takarar wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattijan tarrayar Najeriya, da kuma barrista A'isha Ali Tijjani yar gwaggarmayar kare hakkokin bil'adama musamman mata, sun bayyana yadda za a yi amfani da ilimi wajen cimma wannan burin da kuma yadda suke ganin za a iya tsarkake tsarin damokaradiya. Bakin sun kuma bayyana amfanin hamayya a mulkin damokaradiya.
Saurari cikakken shirin.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.