Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Soyayya Ta Sa Budurwa Cinnawa Kanta Wuta, Kashi Na Biyu-Octoba, 10, 2019


Alheri Grace Abdu

Makonni biyu da suka gabata muka fara kawo maku rahoto kan halin da wata budurwa da ake kira Aisha take ciki , wadda take kwance a wani asibiti dake garin Gusau na jihar Zamfara, domin cinnawa kanta wuta da tayi bayin jin cewa sauraryi da take matukar kauna ba zai iya aurenta ba sabili da talauci.

A hirarshi da shirin Domin Iyali, kawun yarinyar ya bayyana cewa, basu taba sanin matukar soyayyar dake tsakanin wannan saurayi da budurwarsa zai kai ga ta nemi hallaka kanta ba. ya kuma yi alkawarin cewa, idan Allah ya bata lafiya za a daura masu aure ko ta wanne hali.

Shi kuwa a nashi bayanin, saurayin yace, ko a gadon asibitin idan an yardar mashi zai auri Aisha ya kuma ci gaba da jinyarta har Allah ya bata lafiya.

Saurari hirarrakin masu sosa rai da shirin ya yi da su duka.

Soyayya Ta Sa Budurwa Cinnawa Kanta Wuta, Pt2-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:13 0:00  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG