Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Za A Rufe Makarantun Da Ake Gallazawa Mutane A Najeriya, Oktoba,17, 2019


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Shugaban Nageriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe makarantun Islamiyan da aka gano suna gasawa mutane akuba. Wannan ya biyo bayan ceto daruruwan mutane da suka hada da kananan yara saba’in da bakwai a garin kaduna da kuma na baya bayan nan bore da wadansu dake irin wannan makarantar dake garin Daura suka yi ranar Lahadi bayanda wuya ta ishesu.

A cikin hirarsu da wakilinmu Umar Faruk , kakakin shugaba Muhammadu Buhari Garba Shehu ya bayyana matsayin shugaban kasar da cewa ba za a lamunci wannan aika aikar ba, kuma za a hukumta duk wadanda aka samu da laifi domin ya zama ishara ga saura.

Ita ma a nata bayanin, kwamishinar mata da inganta rayuwar al'umma ta jihar Kaduna, Hafsat Mohammed Baba tace gwamnatin jihar ta tsara yadda za a kula da mutanen da aka ceto.

Saurari cikakken shirin

batun gallazawa kangararru a makarantun Islamiya-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:35 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG