A wannan shirin Domin Iyali da ya kasance na farko a shekara ta dubu biyu da goma sha tara, yau Alhamis uku ga watan Janairu, Shirin Domin Iyali ya nemi sanin abinda yafi tsonewa al’umma ido da kuma inda suke butakar gani gwamnati ta bada karfi bana. Mun kuma nemi jin ta bakin al’umma a kasashen Najeriya, Nijar, Ghana da kuma Kamaru.
Ga abinda ‘yan Najeriya da Ghana ke gani idan an yi zai inganta rayuwar iyali da ci gaban kasa. Sai mako mai zuwa mu nufi kasashen Kamaru da kuma Nijar.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.