Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Cika Shekaru Biyar Da Sace 'Yammatan Chibok, Afrilu 18, 2019


Grace Alheri Abdu

Yayinda ake cika shekaru biyar da sace 'yammatan Chibok, da har yanzu kungiyar Boko Haram da ta sace su take rike da 'yammata dari da goma sha biyu daga cikin 'yammata dari biyu da saba’in da shida da ta sace a makarantar su, kungiyar kuma take ci gaba da rike Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren garin Dapchi bayan sakin sauran dalibai sama da dari da aka sace su tare, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin gaza ceto ‘yammatan tare da sake yin alkawarin ceto su.

Sai dai kungiyar fafatukar ceto 'yammatan da taken Bring Back Our Girls, tace gwamnatin tana ci gaba da kura kurai dangane da wannan batun, musamman ta fannin hulda da iyayen yammatan.

Saurari shirin domin karin bayani

Shekaru 5 da sace 'yammatan Chibok-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:23 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG