Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali-An Kama Matar Da Ta Kulle Yaro A Dakin Kare A Lagos, Satumba,05, 2019


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Hakalin al'umma ya tashi da ganin wani faifan bidiyo da aka yayata a kafofin sada zumunta inda aka ga wata mata tana dukan wani karamin yaro da bel, daga shi sai wando, daga nan ta tunkuda shi da kafa zuwa dakin kare ta kulle shi tayi tafiyarta.

Makonni biyu da suka gabata rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta gurfanar da wata mace da ake zargi da cin zarafin wani karamin yaro dan agola, da aka yayata a shafunan sada zumunta, inda aka ganta tana dukan yaron tana janshi da karfi, daga nan ta kulle shi a dakin kare. Abinda yake kara haska filita kan cin zarafin kananan yara da ake ci gaba da yi a wannan karnin musamman wadanda ake dauka riko.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, kan wannan lamarin, DSP Bala Elkana Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Lagos ya bayyana cewa, tuni aka kama wannan matar bayan samun labarin, za a kuma ci gaba da tsare ta har zuwa lokacin da za a kammala bincike a gurfanar da ita ga kotu.

Wannan lamarin dai ya jawo suka a ciki da wajen Najeriya a daidai lokacin da kasar ke fama da kalubalai da dama da suka hada da matsalar tsaro..

Cin zarafin karamin yaro a Lagos:10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:04 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG