Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali-Magidanci Ya Yiwa Kawar 'Yarshi Ciki-Kashi Na Biyu-Agusta,22, 2019


Alheri Grace Abdu

Makon da ya gabata shirin Domin Iyali ya fara gabatar da hira da shirin ya yi da uwar wata yarinya 'yar shekaru goma sha uku dake zaune a garin Misau jihar Bauchi, wadda wani mahaifin abokiyarta a makaranta ya yi mata ciki bayan ya shafe sama da shekaru biyu yana mata fyade da tunanin cewa shekarunta basu kai da zata iya daukar ciki ba.

A Yau shirin ya yi hira da wan yarinyar wanda shima muka saya sunansa wanda ya bayyana cewa bayan an zauna da mai unguwarsu wanda ya kansace limamin garin da kuma wa a wajen wanda ya yiwa yarinyar ciki, da kuma kungiyar Hizba, aka cimma yarjejeniya a rubuce da mutumin cewa zai dauki nauyin dawainiyarta ya kuma amince zai aure ta amma daga baya suka zame aka bar yarinyar a rana.

Ga bayanin da ya yiwa wakilinmu Abdulwahab Mohammed.

Yiwa karamar Yarinya Fyade A Misau; Pt2-10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:22 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG