Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali, Nuwamba 29, 2018, Sace Yammata A Diffa,Nijar


Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu

Ranar asabar da ta gabata, wadansu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da wasu ‘yan mata 15 a kauyukan da’irar Tumur dake yankin Diffa da dare, baya ga wannan kuma aka yi garkuwa da wadansu kananan yara biyu a birnin Kwanni da wadanda suka sace su suka bukaci a biyasu naira miliyan goma, kwatankwashin sefa miliyan goma sha biyar, a matsayin kudin fansa, sai dai aka dace, aka saki wadannan yara a daren litinin. yayinda kuma rahotannin yammacin litinin ke nuni da cewa, biyu daga cikin ‘yan matan da aka sace a daren juma’a 23 ga wata sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Wannan lamarin da yayi matukar tayar da hankalin jama’a, ya kuma sa Al’umomi kira ga hukumomi su dauki matakin magance matsalolin Boko Haram da suke kara zafafa kai hare hare da aikata wasu miyagun ayyuka a ‘yan kawanakin nan a yankin Diffa inda satar mata da yara kanana domin neman kudin fansa ke kokarin samun gindin zama.

Lamari na baya bayan nan ya faru ne kwanaki 500 bayan sace rukunin farko mai kunshe da mata da yara kanana kimanin 39 a kauyen Ngalewa abinda ‘yan majalisar dokoki daga mazabar wannan yanki suka yi tur da shi

Kungiyoyin kare hakkin mata sun bayyana kaduwa da yadda wannan al’amari ke kara tsananta duk kuwa da cewa doka ta haramta cin zarafin dan adam a Nijer.

Matsalolin ta’addanci a Jamhuriyar Nijer wani abu ne da ya mayar da dubban yara marayu wadanda aka hallaka iyayensu a filin daga ko wadanda aka tarar a cikin gida.

Rahotannin yammacin litinin 26 ga watan Nowamba na cewa, biyu daga cikin ‘yan matan da aka sace a daren juma’a 23 ga wata sun yi nasarar tserewa daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Zaman dar dar din da aka shiga a yankunan da kungiyoyin ta’addanci ke cin karansu ba babbaka ya sa wasu iyaye a karkara soma dari darin sanya ‘yayansu aikace aikacen da a can baya yara musamman ‘yan mata ke yi domin walwalar iyali .

Abinda shirin na yau zai ya yi nazari ke nana kai a wannan makon.

Saurari cikakken shirin

Sace 'Yammata a Nijar-10:30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:32 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG