Wani batu dake ci gaba da daukar hankalin al’umma a kasashen duniya shine, babban zaben kasa a Najeriya, wanda mata suke bayyanawa a matsayin koma baya, kasancewa da dama sa suka nemi tsayawa takara basu kai labari ba.
Ta haka muka gayyaci mata masu ruwa da tsaki a zauren taron ofishinmu dake birnin tarayya Abuja yayin dauko rahotannin zaben, da nufin nazarin yadda za a iya samu mata su bada gudummuwa a tsare tsaren da zasu shafi rayuwarsu da ci gaban kasa.
Saurari tattaunawar
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.