Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Canza Sheka na Cigaba da Kadawa a Jihar Adamawa


PDP
Guguwar canza sheka ta sake kadawa a jihar Adamawa inda wasu kusoshin jam'iyyar APC suka koma jam'iyyar PDP.

Wadanda suka canza sheka sun hada da Injiniya Marcus Natina Gundiri wanda ya taba tsayawa takarar gwamnan karkashin jam'iyyar ACN da ke cikin hadakar da ta haifi APC. Sun ce su tare da magoya bayansu fiye da dubu goma sun canza sheka zuwa PDP bisa ga zargin rashin rike amana da yin adalci. In ji su irin mutanen dake cikin APC ba zasu iya rike amana ba domin haka su ba zasu iya aiki da su ba. Wata mai magana da yawun PDP ta gayawa Gundiri cewa tun da ya dawo PDP za'a zabeshi.

Jam'iyyar APC ta mayarda martani inda sakatarenta na yada labarai Alhaji Salihu Baba Ahmed ya yi fatali da batun canza shekar. Yace haka siyasa ta ke ka fita daga wannan jam'iyyar zuwa waccan. Ya ce su basu razana ba da fitar tasu. Yace idan mai babbar riga ya fita daga jam'iyyar APC basa jin tsoro. Abun da zai tsoratasu shi ne fitar talaka daga jam'iyyarsu.

Yayin da ake wannan dambarwar siyasar sai gashi gwamnan jihar na buga kirji cewa jam'iyyar APC zata lashe zaben jihar inda zasu kawar da duk azzalumai.

Ga karin bayani.
Guguwar Canza Sheka na Cigaba da Kadawa a Jihar Adamawa - 3:22
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG