Accessibility links

Gwamna Wamako na jihar Sokoto ya soki gwamnatin tarayya da shirya shagulgula kan cika shekara dari da kafa kasar yayin da 'yanbindiga ke kashe mutanenta.

Gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakarda Wamako yayi fira da manema labarua a Abuja inda ya soki gwamnatin tarayya da kakkausa lafazi domin shagulgulan bikin cika shekara dari da kafa kasar yayin da 'yanbindiga ke kashe mutane a arewa maso gabashin kasar.

Wannan jawabin na gwamna Wamako ya zo daidai lokacin da 'yan kasa ke ta kiraye-kiraye cewa duk masu fada a ji kamar shi shugaban kasa da wasu yakamata su je jihohin Adamawa da Borno da Yobe su jajantawa mutanen jihohin domin irin bala'in da ya addabesu. Yakamata su jajanta masu kan rayukan da suka yi asara da daukan sabbin matakan da zasu kawo karshen asarar rayuka.

Gwamna Wamako yace bisa gaskiya Najeriya kasa ce mai ban tausayi. Yace maimakon shagali zaman makoki yakamata kasar ta yi. Abun da yakamata shugaban kasa yayi shi ne yana jihohin dake fama da ta'adanci ba wai yana Abuja yana barci ba. Idan da yana da masu bashi shawara na kwarai kamata yayi a dage taron kasa da duk wani shagali har sai an samu zaman lafiya a kasar. Jama'a suna cikin makoki a ce kuma ana bikin cika shekaru dari da kafa kasar. Gwamnan yace babu abun yin biki a kai yanzu.

Dangane da irin abun da su gwamnoni zasu iya yi sai gwamnan yace nasu su yi addu'a su kuma bada shawara. Gwamnatin tarayya ke da jami'an tsaro domin haka harkar tsaro ba hakinsu ba ne. Abun da yakamata a yi shi ne duk wani babban jami'in tsaro a ce yana Adamawa ko Yobe ko Borno. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kamata yayi a ce yana Maiduguri ba Abuja ba. Amma maimakon hakan duk sun tare a Abuja suna jin dadi bayin Allah kuma na can ana kashesu kamar kiyashi.

Ga cikakken rahoto.

XS
SM
MD
LG