Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Dorian Na Kara Barazanar Zubar Da Ruwan Sama Mai Yawa


Guguwar Dorian

Masana a Amurka, sun yi hasashen cewa mahaukaciyar guguwar nan da aka wa lakabi da “Dorian” ba za ta sauka kai-tsaye kan jihar Florida ba, amma duk da haka, an gargadi jama’ar yankin da su cigaba da zama cikin shirin ko-ta-kwana.

Kwararru sun ce, guguwar na kara zama mai karfin gaske, za ta kuma rabi jihohin Florida da Goergia a daren Talata zuwa wayewar garin Laraba, sannan za ta zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin North Carolina da South Carolina dauke da guguwa mai karfin gaske.

A cewar gwamnan jihar ta North Carolina, Roy Cooper, “lura da cewa ana fargabar guguwar za ta kara saurin tafiyarta, lokacin da ake da shi na kimtsawa na korewa.”

Guguwar wacce tuni ta sauka kai-tsaye akan yankin Bahamas, ta lalata akalla gidaje dubu-goma-sha-uku a kiyasin farko da aka yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG