Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar "Dorian" Ta Kashe Mutum 5 A Tsibirin Abaco Na Bahamas


Mahaukaciyar guguwar da aka yi wa lakabi da "Dorian" da ba'a taba ganin irinta ba a cikin shekaru 84, ta doshi wasu jihohi a Amurka.

Mutane kalilan ne kadai su ka iya barci a Bahamas a daren jiya, bayan da mahaukaciyar guguwar nan mai lakabin Dorian ta dira kan tsibirin Grand Bahama, ta yi ta wargaza shi da iska mai karfin gaske, da kuma ruwa kamar da bakin kwarya.

Firaministan Bahamas, Hubert Minnis, ya tabbatar da mutuwar mutane akalla biyar a tsibirin Abaco na Bahamas, ya na mai bayyana barnar da ta auku a arewacin Bahamas a matsayin, “abin da ba a taba gani ba, kuma mai matukar yawa.”

Dorian ce mahaukaciyar guguwa mafi karfi da ta taba dira kan doran kasa cikin tsawon shekaru 84, kuma ita ce mafi muni da ta taba dira kan Bahamas.

Firaminista Minnis ya ce dogarawan tsaron gabar Amurka sun iso Abaco don su taimaka da ayyukan ceto, amma dole a dakatar da ayyukan ceto mafiya yawa har sai bayan guguwar ta yi sauki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG