Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwar Irma: Miliyoyin Mutane Sun Rasa Wutar Lantarki a Florida


Al'umar jihar Florida da suka tserewa guguwar Irma, yayin da suke jira a bude hanyoyin da za su koma gidajensu, ranar 11, Satumba 2017.
Al'umar jihar Florida da suka tserewa guguwar Irma, yayin da suke jira a bude hanyoyin da za su koma gidajensu, ranar 11, Satumba 2017.

Mazauna tsibirin  da ke kudancin Florida inda  mahaukaciyar guguwar nan ta Irma ta yi  wa mummunar illa, yanzu  haka ba  za su  iya  dawo  wa  gidajen  su ba har  na tsawon makonni, kamar yadda  fadar  shugaban Amurka ta White  House  ta  fada jiya Litinin.

Mai baiwa shugaba Donald Trump shawara a harkokin tsaron cikin gida Tom Bossert, ya ce kafin abubuwa su farfado su koma yadda suke a jihar Florida zai dauki lokaci, domin kuwa guguwar ta lalata gadojin da suka hada cikin birni da sauran bangaren birnin.

Bossert dai yana magana ne bayan da jami'ai a Florida suka kammala dukkan bincikensu tare da auna irin illar da guguwar ta Irma ta yi.

Wannan guguwar dai, bayan da ta kassara arewacin Florida, yanzu ta dangana zuwa jihar Georgia tare da haifar da ambaliya a yankin.

Hakan ya sa yawan gidajen jama'a da abin ya shafa gidajensu suka kasance cikin wannan mawuyacin hali, musammam daga yammacin Florida ta gabar kogin Mexico har ya kai zuwa babban birnin mafi girma a jihar, sai kuma Jacksonville ta gabar Tekun Atlantika.

Jihar Florida dai ita ce jiha ta uku mafi yawan jama’a Amurka, wadda take da kamar mutane miliyan 20, kuma miliyan shidda daga cikin mutanenta ba su da wutar lantarki a sanadin wannan guguwar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG