Accessibility links

Gwamna Adam Oshimole Ya Sami Gagarumar Nasara A Edo.

  • Aliyu Imam

Kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya suke maci. Kungiyar da Gwamna Oshimole yayi wa jagoranci a baya

Bayan yakin neman zabe cike da hayaniya, da suka hada da zargin magudin zabe, jama'a a jihar Edo yanzu suna rawa da sowa akan tituna.

Bayan yakin neman zabe cike da hayaniya, da suka hada da zargin magudin zabe, jama'a a jihar Edo yanzu suna rawa da sowa akan tituna.

Hukumar zabe tace Gwamna mai ci Adam Oshimole, na jam'iyyar 'yan hamayya ya sami babban rinjaye a zaben gwamna da aka yi ranar Asabar.

Masu fashin bake suka ce nasarar da 'yan hamayya suka yi a yankin da ya zame tamkar tungar jam'iyyar dake mulkin kasar PDP, ba alama ce mai kyau ga shugaba Goodluck Jonathan ba.

Jiragen yaki masu saukar ungulu suna ta shawagai a wajajen rumfunan zabe jiya Asabar, da tsammanin za a sami rikici. Dubban sojoji kuma suna sintiri kan tituna da kuma a rumfunan zabe. Amma ba a fuskanci wani tarzoma mai tsanani da aka sami labari ta auku ba.

A safiyar lahadin nan, bayan da aka bayyana sakamakon zaben gwamnan, mutane suka fantsama akan tituna suna rawa ana kuma ruwan sama.

Hukumar zabe ta Najeriya tace Gwamna Oshimole ya sami kashi 73.7 na yawan kuri'u da aka kada, ita kuma jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta sami kashi 22.3. Sauran kashi 4 da ya rage sauran jam'iyyu suka raba tsakaninsu.

Wani manomin doya da rogo, Emmanuel Igbinedon, yace wan nan zaben shine zakaran gwajin dafi a jihar ta Edo.

"Wan nan zabe shine wanda aka gudnar cikin lumana fiyeda ko wanne da aka taba yi. "Kuma wan nan zabe ya koya mana darasin cewa ba a sayen kuri'a".

Kamin zaben, duka jam'iyun biyu suna ta zargin juna na kitsa magudi da tarzoma, wadanda suka hada da hayan masu kisan gilla. Har zuwa lokacinda ake kidaya kuri'u ma, gwamnan jihar ya zargi hukumar zabe cewa da gangan ta makara kai kayan zabe da kuma cire sunayen masu zabe a kundin sunayen masu kada kuri'a. Kuma tayi haka ne tareda hadin bakin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

Wata kungiyar tallafi mai zaman kanta mai cibiya a Abuja tace tayi aiki da dubban masu aikin sa ido a jihar, wadanda suka ce an sami nasarar a zaben da aka gudanar da aka nuna adalci, duk da 'yan matsaloli da aka fuskanta.

Da yake magana, babban darektan kungiyar Clement Nwankwo, yace sakamakon zaben wata babbar koma baya ce ga jam'iyyar dake mulkin Najeriya a tarayya, domin jihar Edo tana cikin yankin "kudu maso kudu", inda daga yankin ne shugaba Jonatahan yake da mafi yawan goyon baya.

"Nasarar da dan takarar ACN ya samu babba ce, kuma ta kasance manuniya kan zubewar farin jinin da shugaba Jonathan yake da shi, inji Nwanko.

'Yan hamayya suka ce nasarar da aka samu ana jiya jingina ta kan wani hadin kai tsakanin 'yan hamayya, kuma sunyi alkawarin zasu hada karfi wajen ganin sun kada Jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa, a 2015.

XS
SM
MD
LG