Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Danbaba Suntai Ya Koma Najeriya


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Gwamnan Jihar Taraba Danbaba Suntai ya koma Najeriya bayan ya kwashe watanni goma yana jinya.

Yanzu dai za'a ce jita-jita ta kare kan gwamnan jihar Taraba Danbaba Suntai wanda ya kwashe watanni goma yana jinya a kasashen waje.

Kimanin watanni goma ke nan da gwamnan Jihar Taraba ya yi hadari da jirgin sama wanda shi ne matukin kafin ya sauka a filin saukan jirage dake Yola lamarin da ya yi sanadiyar mugun rauni da ya samu. Da farko an kaishi kasar Jamus inda ya soma jinya kafin a gangara dashi zuwa Amurka.

Tun lokacin da ya soma jinya akai ta kai ruwa rana kan ko zai iya ma komawa Najeriya. To yau Gwamna Suntai ya sauka a birnin Abuja babban birnin tarayya Najeriya. 'Yan jarida sun yi kokarin samun zantawa da shi amma duk kokainsu ya cutura. Jami'an gwamnati da jami'an tsaro sun mamayeshi suka hana kowa ya yi magana da shi. Sai dai wakilin Muryar Amurka da ya je kusa ya ce bisa duka alamu gwamnan baya iya tafiya sai da taimako.

Bayan ya sauka a Abuja sai ya shiga wani jirgin da ya kaishi Jalingo. A Jalingon ma bata sake zani ba domin ba'a bari ya zanta da 'yan jarida ba. Jami'an tsaro sun kankane wuri suka sa shi a mota sai fadar gwamnatin jihar. Da alamu zai karbi mulki kana ya koma inda ya fito ya cigaba da jinya.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG