Accessibility links

Gwamna Kashim Shettima Na Jihar Borno Ya Ce Allah Zai Saka Ma Wadanda Aka Kai Wa Hare-Hare

  • Ibrahim Garba

Gwamna Kashim Shettima

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce da wadanda su ka kai hare hare kan bayin Allah a Borno, da maharan da ma sauran jama'a, kowa ya san cewa Allah ba fa azzalumin kowa ba ne. Sakayyar Allah ta na nan tafe.

Gwamna Kashin Shettima na jihar Borno ya ce Allah ba azzalumin kowa ba ne, don haka wadanda aka kai masu hare-haren bama-bamai a Maiduguri bas u ji ba ba su gani ba, Allah zai saka masu. Su kuma da su ka kai hare-haren lallai Allah zai hukunta su.

A hirarsa da waklinmu a Maiduguri Haruna Dauda Biu, Gwamna Shettima ya ce ya gaggauta kai ziyara ga wadanda aka kai su asibitoci ne saboda ya nuna masu cewa ya na tare da su.

Ya ce wasu dama ba su da wani jarin kirki amma an hallaka su ko kuma an raunata su, don haka ya zame masa dole ya je ya gansu ya kuma gaggauta taimaka masu. Ya yi kira ga ‘yan jihar su hada kansu komai tsanani daga ‘yan bindigar.

XS
SM
MD
LG