Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Shettima da Shehun Borno Sun Gana da Janaral Babangida


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima a Maiduguri, Mayu 22, 2014. (File Photo)

Gwamnan Borno Kashim Shettima da Shehun Borno Garba El-Kanemi tare da wasu manyan mutanen jihar sun yi wata ganawar siri da tsohon shugaban Najeriya Janaral Ibrahim Badamasi Babangida ko IBB a takaice.

Sun gana da tsohon shugaban ne a gidansa dake Minna babban birnin jihar Neja jiya Lahadi.

Ganawar ta hada da wasu kusoshin jihar ta Borno irin su Sanata Ali Ndume da wasu dattawa.

.Ba'a bar manema labarai shiga dakin ganawar ba da ta dauki tsawon awa guda da rabi amma bayanai sun nuna tana da alaka da sha'anin tabarbarewar tsaro da ya addabi jihar da ma yankin arewacin Najeriya gaba daya musamman a wannan lokacin da zaben shekara mai zuwa ke kara karatowa. Ban da haka lamarin rashin tsaron na kara ta'azzara.

Dattijo, kuma masanin harkokin tsaro da al'amuran yau da kullum, Alhaji Muhammed Danlami yace ba sai gwamnan Borno ya roki a sa baki akan harkar tsaron jiharsa ba domin yaji yana rokon manya su sa baki. Yace an kashe Janaral Shuwa amma har yau babu binciken da aka yi a gano wadanda suka kasheshi.

Alhaji Danlami yace abubuwan sun wuce sanin inda ake. Tabarbarewar tsaro ta wuce Borno. Mutane sun shiga makarantu sun kashe yara.

Wani dan majalisar dattawa Abdullahi Idris Garba ya tabbatar da mahimmancin ganawar. Yace gwamnan Borno yana zgayawa wurin manyan arewa yana neman yadda za'a samu zaman lafiya. Yana zuwa wurin sarakuna kuma zuwa wurin IBB wanda ba karamin mutum ba ne yana da mahimmanci kwarai.

Alhaji Garba ya kara da cewa yunkurin majalisar na neman tsige shugaban kasa yana nan daram. Zasu zauna uku ga wannan watan su yi muhawara akai. Kawo yanzu mutane 180 suka sa hannun a tsige shugaban kuma yana da kwarin gwiwa hakansu zai cimma ruwa.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG