Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Anambra Obiano Ya Kai Karar Malami Wajen Buhari


Gwamna Obiano (hagu) Abubakar Malami (dama) (Facebook/Malami/Obiano)
Gwamna Obiano (hagu) Abubakar Malami (dama) (Facebook/Malami/Obiano)

A ranar Laraba Malami ya fadawa manema labarai cewa mai yiwuwa a saka dokar ta-baci a jihar ta Anambra saboda karin tabarbarewar tsaro da ake gani a yankin.

Gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya Willie Obiano ya kai karar Ministan Shari’a Abubakar Malami fadar shugaban kasar kan kalaman da ya yi na cewa mai yiwuwa a saka dokar ta-baci a Anambra.

Jihar ta Anambra ta kwashe wasu watanni tana fama da rigingimu masu nasaba da ‘yan kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, lamarin da kan kai ga asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Hakan ya sa Malami wanda har ila yau shi ne Babban Atoni janar din kasar, ya fadawa manema labarai a fadar ta shugaban kasa a ranar Laraba cewa, akwai yiwuwar a ayyana dokar ta-baci a jihar ta Anambra idan matsalar tsaro ta ci gaba da dagulewa.

Kalaman Malami na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben gwamna a jihar wanda za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

A kwanan nan hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan yadda rikici ya dabaibaye jihar inda ta nemi da a samar da cikakken tsaro.

Sai dai gwamna Obiano wanda ya ziyarci Buhari a fadarsa a ranar Alhamis ya fadawa manema labarai bayan ganawar cewa bai ji dadin kalaman na Malami ba.

“Kalaman Atoni-Janar din abin takaici ne. Na kuma kai karansa wajen shugaban kasa, don na san cewa batun saka dokar ta-bacin ba ya cikin tsare-tsaren shugaban kasa, domin (Buhari) ya san cewa Anambra na daya daga cikin jihohi masu zaman lafiya a Najeriya sama da shekaru bakwai.”

Gwamna Obiano ya kuma ce zai kira Malami don ya nuna masa rashin jin dadinsa dangane da kalaman da ya yi kamar yadda rahotanni daga Najeriyar suka nuna.

XS
SM
MD
LG