Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Adamawa ya ce Gwamnatinsa Zata sa Kafar Wando Guda da Yan Bata Gari


Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Gwamnatin jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya ta gargadi sarakunan yankunan Numan, Demsa da kuma Lamurde da su gaggauta kawar da kungiyoyin matasa na yan bangan dake kafa shingaye.

Kananan hukumomin uku dai a yan kwanakin nan sun yi fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin makiyaya da manoma yan kabilar Bachama, lamarin da ya jawo asarar rayuka fiye da dari, kuma wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin nemo bakin zaren maido da kwanciyar hankali a yankunan.

Wannan gargadi dai ya biyo ne bayan wasu rahotanni dake cewa yayin da ake kokarin maido da zaman lafiya a yankunan da rikicin Fulani da al’umman Bachama ya shafa, yanzu haka akwai wasu kungiyoyi dake fakewa da sunan banga suna fidda mutane a mota suna kissan dauki dai dai, batun da gwamnati tace ba zata kyale ba.

Gwamnan jihar Adamawan Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, wanda ya nuna kaduwar gwamnatin jihar dangane da wannan sabon lamari, ya gargadi sarakunan yankin da su dakatar da wadannan kungiyoyi, ko kuma duk wanda aka kama ya gamu da fushin hukuma, komin matsayinsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG