Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan jihar Bauchi ya bayyana takaicin sake bullar shan inna


ປະຊາຊົນພາກັນຢືນເບິ່ງ ຊິ້ນສ່ວນຂອງເຮືອບິນໝາກປິ່ນ ຂອງສາຍການບິນລາວ ທີ່ຕົກລົງສູ່ແມ່ນໍ້າຂອງ ຢູ່ປາກເຊ ເມື່ອວັນທີ 16 ຕຸລາ 2013.

Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda ya bayyana damuwa dangane da sake bullar kwayar cutar shan inna a jihar.

Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda ya bayyana damuwa dangane da sake bullar kwayar cutar shan inna a jihar.

Gwamna Yuguda ya bayyana haka ne yayin kaddamar da shirin allurar rigakafin shan inna ta shekara ta 2012 .

Ya bayyana cewa, za a dauki dukan matakan da suka kamata na ganin an shawo kan yaduwar cutar a jihar. Bisa ga cewarshi, an shafe shekaru biyu ba tare da samun wani yaro dauke da kwayar cutar shan inna ba a jihar Bauchi, ya kuma ce za a hada hannu domin ganin hakan ta ci gaba duk da koma bayan da aka samu ta wajen sake bullar cutar.

Gwamna Yuguda yace an sami bullar cutar a jihar ne sabili da kaura da jama’a ke yi daga wadansu jihohi musamman jihohin dake makwabta. Ya kuma yi kira ga iyaye su bada goyon bayan da hadin kai yayinda ya dokaci mata su tallafawa yunkurin gwamnati ta wajen wayar da kan abokan zamansu da ‘ya’ya da kuma makwabta dangane da muhimmancin allurar rigakafin.

Gwamnatin jihar Bauchi dai ta kara kaimin rigakafin ne sakamakon samun wadansu kananan yara guda biyu da aka yi dauke da kwayar cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG