Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Zabi Pence a Matsayin Abokin Takara


Trump tare da Mike Pence

Mutumin da ake ganin shi jam’iyar Republican za ta tsayar dan takarar shugaban kasa a Amurka, Donald Trump, ya zabi gwamnan Indiana, Mike Pence a matsayin abokin takararsa.

A 'yan kwanakin ana ta yaya ta cewa Trump zai zabi Pence a mukamin mataimakin shugaban kasa, sai kuma Trump din ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter da safiyar yau Juma'a.

"Ina mai matukar farin cikin bayyana zabin gwamna Mike Pence a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa." Trump ya rubuta a shafin nasa na Twitter.

A gobe Asabar Trump ya ce zai gudanar da wani taron manema labarai domin ya gabatarwa jama'a zabin nasa.

Pence ya kasance mutum ne mai ra'ayin mazan jiya da ya fito daga jihar Indiana da ke yammacin tsakiyar Amurka.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG