Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan jihar Kebbi ya ci alkawashin daukar mataki kan masu gunguntar da shirin rikagafin shan inna


Maikacin gwamnati tana bama yara maganin cutar shan inna

Gwamnan jihar Kebbi yace zai shiga kafar wando daya da masu kawo cikas a yaki da shan inna

Gwamnan jihar Kebbi Sa’idu Dakingari ya ci alwashin shiga kafar wando daya da duk wani shugaban karamar hukuma ko basaraken gargajiya da yaki ba gwamnatinshi hadin kai a yunkurin shawo kan cutar shan inna a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar alhaji Isma’ila Sambawa, wanda ya wakilci mataimakin gwamnan, Alhaji Ibrahim K. Aliyu a wajen kaddamar da rigakafin shan inna da aka gudanar a karamar hukumar Jega ne ya bayyana haka.

Sambawa ya bayyana cewa, sabili da makudan kudin da gwamnatocin jihar da na tarayya da kuma cibiyoyin agaji suke kashewa kan aikin rigakafin, da kuma muhimmancin lafiyar al’umma ga gwamnatin jihar, yasa ba za a bari shirin ya gamu da cikas ba.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma su fito da ‘ya’yansu a yi masu rigakafi a kowanne lokaci, yayinda ya kuma yi kira ga jami’an aikin jinya su gudanar da aikinsu tsakani ga Allah.

A cikin jawabinshi, jami’in cibiyar asusun kananan yara –UNICEF Rabi’u Musa ya bayyana gamsuwa da matakan da gwamnatin jihar Kebbi ta dauka na yaki da cutar shan inna da kuma nasarorin da aka samu.

Sarkin Kabbin Jega, Alhaji Mohammed Arzika a nashi bangaren, ya yi alkawarin bada hadin kai da goyon bayan domin ganin nasarar shirin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG