Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Ondo Ya Kamu Da Cutar Coronavirus


Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu

Gwamnan jihar Ondo a Najeriya, Rotimi Akeredolu ya kamu da cutar Covid-19. Ya bayyana hakan ne a kan shafinsa na Twitter a yau Talata.

Ya ce "a yau gwaji ya nuna cewa ina dauke da Covid19. Ban nuna alamun cutar ba kuma har na fara kilace kaina."

Ya kuma bukaci da a taya shi da addu'ar samun sauki. A cewar gwamnan, zai ci gaba da aikinsa.

A cikin faifan bidiyon da ya wallafa a Twitter Akeredolu ya ce an yi masa gwajin cutar ne bayan da ya gama jinya sakamakon cutar Malaria.

Gwamnan ya bayyana cewa wani gwamna ne ya ba shi shawarar zuwa a yi masa gwajin cutar, a wajen taron majalisar zartarwa na jam'iyyar APC a Abuja.

A cikin kwanakin nan dai gwamnoni da dama sun kamu da cutar ta Covid-19 a Najeriya.

Ya zuwa yanzu fiye da mutum 25,000 ne cutar ta kama a kasar.

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG