Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Oyo Yace Ma'aikata Su Nemi Gafara Domin Sulhu


Dalibai masu zanga zanga da ma'aikata suka harzukasu

Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi yace idan ma'aikatan kwadagon gwanatin jihar na son su yi sulhu da gwamnatin dole ne su nemi gafara game da wargaza taron masu ruwa da tsaki da aka yi akan ilimi ko kuma su biya diyya kan kayan gwamnati da aka lalata

An lalata kayan gwamnati sakamakon zanga zangar da daliban makarantun sakandare suka yi a kwanakin baya.

Gwamna Ajimobi ya yi furucin ne a lokacin da yake tattaunawa da wani radiyo mai zaman kansa a Ibadan fadar gwamnatin jihar. Gwamnan yace ba zata yiwu ba mutane su lalata kayan gwamnati, su ki biya, kana su ki neman gafara game da ta'asar da suka tafka.

Gwamna Ajimobi yace su ba zasu amince da tada zaune tsaye ba a jihar. Da ya juya kan bukatun 'yan kwadagon na a biyasu albashi da alawus alawus da suke bin gwamnati, sai ya ce ahalin yanzu basu da isassun kudi kuma basu kadai ba ne ke bin gwamnatin bashi. Yace akwai 'yan siyasa amma basu shiga yajin aiki ba.

Mr. Ajimobi yace yajin aikin 'yan kwadagon bai yi tasiri ba. Yace sun kira yajin aiki amma kananan ma'aikata ne suka shiga yajin aikin. Manyan ma'aikata suna aiki kuma kome na tafiya daidai. Yace ya mika sunayen sabbin kwamishanoni don majalisa ta tantancesu. Kafin mako mai zuwa zasu fara aiki don jihar ta cigaba. Saboda haka yace yajin aikin tamkar aikin banza ne harara a duhu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

XS
SM
MD
LG