Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Taraba, Dickson yace yana kan bakansa akan batun tattance baki da suke shiga jiharsa.


TARABA: Gwamnan Jihar Taraba Arch Dickson Isyaku
TARABA: Gwamnan Jihar Taraba Arch Dickson Isyaku

Da yake yiwa sashen Hausa na Muryar Amurka bayani a kan wannan batu, Gwamnan Jihar Taraba Sanata Darrius Dickson yace wani lokaci gwamnati zata hangi abu daga nesa amma mutane basu gani ba. Yace ba wai suna kyamar baki, dole duk wani gari da zai girma sai ya bari baki sun shigo. Amma kuma yace idan bako zai shigo da fitina dole ne ka tashi tsaye. Kowa na son bakon arziki haka zalika gari ba zai samu arziki ba idan ba baki a ciki amma dole ne a lura da bakin da suke shigowa, idan zasu tada zune tsaye ne to wajiinka ne ka dauki matakan tsaro.

Gwanma Darrius yace dalilin haka ne a duba lamarin, ganin yanda ake fada a ko ina da kuma yarda mutane ke kwarara a jihar ba kamar yadda aka saba ba,dole ya ke kawo tsoro.

A baya dai gwamnatin jihar Tarabar ta sha kakkausar suka daga kungoyoyi dake kare yancin Bil Adama na tauyawa baki yan kasa yancin walwala da zama a duk wani bangare na Najeriya da suka zaba.

To amma sakamakon da matakin tattance baki dake kwarar jihar Taraba ke haifarwa a yan kwanakin nan ya sa masu sukar matakin, sun soma ganin fa’idarsa inji Gwamna Darrius Dickson.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG