YOBE, NIGERIA - Ana zargin cewa dai wani soja ne ya kashe malamin a hanyar Gashuwa, har kuma ya kwace motarsa bayan ya kashe shi.
Amma mutanen kwayen ne suka shaida wa jami’an tsaro wadanda suka kama wannan sojan da wani soja na biyu, wanda ake zargi da taimaka masa.
A halin yanzu dai sojojin guda biyu suna hannun ‘yan sanda, ana kuma ci gaba da bincike akan su.
An kashe Malamin dai bayan an harbe shi ne da bindiga bayan da sojan ya nemi ya rage masa hanya.
Mai magana da yamun gwamnatin Jihar Yobe Alhaji Mamman Muhammed ya ce dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki na bai wa yaran Malamin su biyu aiki, matakin kokari ne na tallafawa iyalansa, musamman ganin cewa yaran sun gama karatun babbar Jami’a.
Ya kara da cewa wannan hanya ce don su ci gaba da samun hanyar ciyar da iyalansu.
Muryar Amurka ta tuntubi kanin marigayin, ya kuma shaida mana cewa suna farin ciki da wannan mataki da gwamnatin Jihar ta dauka.
Saurari rahoton ciki sauti daga Haruna Dauda Biu: