Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Kaduna Ya Ce Babu Dan Takara Dan Arewa da Ya Fi Karfin Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Yayinda gwamnonin jihohin arewa na jam'iyyar APC ke mikawa shugaban kasa tikitin sake tsayawa zabe a shekarar 2019, sauran jam'iyyu ma suna shirin shiga zaben duk da ikirarin da gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya yi na cewa babu wani dan arewa da zai iya tsayawa da Buhari takara ya kai labari gida

A cewar gwamna Nasiru El-Rufai lokaci bai yi ba da shugaban kasa zai ayyana takarar amma kuma su gwamnonin shi suke marawa baya.

Inji Gwamna Nasiru El-Rufai, shugaban kasa ya ce an zabeshi ne ya yiwa kasar aiki har zuwa shekarar 2019, kuma abun da ya sa gaba ke nan. Yace lokacin da zai ce zai yi zaben ko ba zai yi ba bai zo ba.Gyaran Najeriya ne ya sa a gabansa, inji El-Rufai.

Gwamnan Rufai ya ci gaba da cewa wannan zamanin na Buhari ne. Babu wani dan arewa da zai tashi a siyasance ya fi karfin Buhari sai dai rananar da Buhari ya ce ya daina siyasa.

Amma wani matashin dan siyasa daga Adamawa, Adamu Garba ya kushewa ra'ayin gwamnonin kuma ya kalubali tsoffin 'yan siyasa saboda shi zai tsaya takarar shugaban kasa.Adamun mai shekaru 35 a duniya yanzu ya ce Buhari yana da amana amma bai dauki hanyar gyara Najeriya ba. Injishi, haka ma masu shekaru irin nasa basirar gyara ta wuce masu.

Baba Shehuri, karamin ministan ayyuka baya shakkar sake samun nasarar Buhari a zaben 2019 saboda shugaba ne da baya sata baya cutar jama'a duk wanda ya yi takara da shi zai fadi sai dai idan talakawa ne suka yi canji.

Ga Nasiru Adamu da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG