Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Oyo Baya Adawa da Mutumin Jiharsa da Buhari Zai Nada Minista


Shugaba Buhari wanda ya sa sunan Adebayo Shitu daga jihar Oyo cikin jerin sunayen ministocin da zai nada

Biyo bayan jita-jita da mutanen jihar Oyo keyi akan cewa baya son wanda shugaba Buhari ya dauko daga jihar zai nada minista ya sa gwamnan ya karyata zargin.

Gwamnan jihar Abiola Ajimobi yace shi kam baya adawa da zabin shugaban kasa daga jiharsa na wanda yake so ya nada minista, wato Barrister Adebayo Shitu.

Gwamnan yana jawabi ne a lokacin da kungiyoyin 'yan kasuwa, mata , matasa, dalibai, shugabannin addinai da dai sauransu dake dauke da kwalaye masu rubuce rubuce domin nuna goyon bayansu ga Adebayo Shitu. Su wadannan kungiyoyin sun yi wata zanga zanga ne cikin birnin Ibadan.

Jagoran zanga zangar Mr. Bashiru Alade yace Adebayo Shitu mutum ne nagari wanda ba'a taba samun shi da wani laifi ba. Yana da mutunci da adalci da ilimi da kuma tsare gaskiya. Mutum ne da ya dace da duk wani canji da ake son samu.

Shugaban matasa Mr Daramola Abiola yace Mr Shitu mutum ne da ba'a taba kamashi da cin hanci ba.Yace ba'a taba samunshi da yin rubda ciki da dukiyar jama'a ba kuma ba'a taba kai kararsa ga hukumomin EFCC ko ICPC ba.

Gwamnan ya yi watsi da jita jitar cewa baya goyon bayan Adebayo Shitu. Yace tunda shugaba Muhammad Buhari ne ya mika sunansa ba zai yi adawa dashi ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

XS
SM
MD
LG