Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Yi Watsi Da Mu - ‘Yan Gudun Hijra


Najeriya 'yan gudun hijira a Nijar, Mayu 6, 2015.

Tun bayan da Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya, dubban mutane ne suka rasa rayukansu kana wasu miliyoyi suka fice daga muhallansu.

Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijra warwatse a sassa daban daban na Najeriya inda su ke zama a yanayi mara kyau kuma a mafi yawan lokuta a cikin kunci.

Abuja, babban birnin Najeriya, na daga cikin ire-iren wuraren da ke zama mafaka ga dubban ‘yan gudun hijran.

Yayin da gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin an kaiwa wadanda hare-haren suka raba muhallansu dauki a jihohin da ke arewa maso gabashin Najeriya da suka hada da jihohin Borno da Yobe da Adamawa, wadanda ke zaune a Abuja na zargin gwamnati da nuna halin ko in kula da su.

Kusan dukkanin wuraren da ‘yan gudun hijrar da ke Abuja da suka hada da Kuje da Ako da Area One da Deidei da sauransu, sasanoni ne da suka kafa da kansu.

Sai dai Darektan hukumar ba da agajin gaggawa na hukumar rsehen Abuja, Abbas Idris, ya ce batun cewa an yi watsi da su ba gaskiya ba ne.

“Muna iya kokari muga cewa mun dadada musu, muna kula da su, muna kuma janyo kungiyoyi masu zaman kansu domin su zo su ba da tasu gudunmuwa.” In ji Idris.

Daga cikin irin halin kakanikayi da ‘yan gudun hijrar ke fuskanta a sasanonin da su ke, akwai batun matsuguni da wajen wanka da rashin samun kaiwa ga asibiti da kuma uwa uba abin sakawa a baka kana da rashin makarantu ga ‘ya’yansu.

Domin jin karin bayani kan irin halin da masu juna biyu ke ciki da kuma tsokacin da jami’an kiwon lafiya su ka yi, saurarri wannan rahoto na Hassan Maina Kaina akilinmu a Abuja ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG