Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno - Osinbajo


 Farfasa Yemi Osinbajo , Mukaddashin Shugaban Najeriya
Farfasa Yemi Osinbajo , Mukaddashin Shugaban Najeriya

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin ta ceto malaman Jami'ar Maiduguri da ma'aikatan kamfanin NNPC da wani bangaren Boko Haram yake garkuwa da su.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta na kokarin ganin an kubutar da mutanen da ke hannun 'yan kungiyar Boko Haram da aka kamasu a lokacin da suke binciken albarkatun man fetur a jihar Borno.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wani kamfanin sarrafa shinkafa a birnin Arugungu da ke jihar Kebbi.

Mukadasshin shugaban kasan ya ce mutanen sun sadaukar da rayukansu domin yi wa kasa aiki saboda haka tsaro da lafiyarsu, ya rataya a wuyan gwamnati.

A makon da ya gabata ne ne 'yan Boko Haram suka yi wa ayarin mutanen masu binciken man fetur daga Jami'ar Maiduguri da ma'aikatan NNPC kwantan-bauna a jihar Borno.

Lamarin ya kai ga asarar rayukan sojojin Najeriya da wasu 'yan sintiri na sa-kai ko kuma 'yan Civian JTF.

Ga rahoton Murta Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG