Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 34 A harin Da Aka Kai Kudancin Kaduna


‘Yan Bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

'Yan fashin daji a arewacin Najeriya.

Kwana biyu da kai harin da 'yan-bindiga su ka yi a wasu garuruwan karamar hukumar Kaura da ke kudancin Kaduna, gwamnatin jihar ta fitar da sunayen mutanen da aka kashe da kuma asarar dukiyar da aka yi.

KADUNA, NIGERIA - A ranar Lahadi ne dai 'yan-bindiga su ka shiga garuruwan Tsonje, Agban, Katanga da Kadarko da ke karamar hukumar Kaura a Kudancin Jihar Kaduna su ka kashe mutane da dama.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta tabbatar kashe mutane 34 ciki har da sojoji biyu, mutane bakwai kuma sun jikkata yayin aka kone gidaje sama da 200 da shaguna 32.

Duk korafin da wasu kan yi game da fitar da sunayen mutanen da ake kashewa da gwamnati ke yi, masani kan harkokin tsaro Dr. Yahuza Ahmed Getso ya ce hakan ba zai taba zama matsala ba.

Tuni dai ganin munin wannan hari ya sa majalissar malamai da limamai ta Jihar Kaduna jajantawa al'ummar tare da jawo hankali don neman mafita, kamar dai yadda babban sakataren majalissar Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya fada.

Duk lokacin da irin wannan hari ya auku gwamna Nasuru Ahmed El-rufa'i ya kan jajanta kamar dai yadda ya yi a lokacin kaddamar da rahoton tsaro a farkon wannan shekara.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dan-masanin birnin Gwari Alhaji Zubairu Abdurra'uf Idris ya ce, al'ummar birnin Gwari na bukata gwamnatin jihar Kaduna ta yi masu irin wannan sakon jaje da juyayi a kamar yadda ta ke yiwa sauran bangarori.

Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

An Kai Wani Mummunan Hari A Jihar Kaduna Da Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 34
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

XS
SM
MD
LG