Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Najeriya Sun Tarwatsa Wasu ‘Yan Bindiga Da Suka Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Jihar Neja


Gamayyar Jami’an tsaron Nigeria sun samu nasarar tarwatsa wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a wani ofishin ‘yan sanda na jihar Nejan Najeriya.

NIGER, NIGERIA - Wannan dai yana zuwa kwana daya bayan da wasu ‘yan bindigar suka hallaka wani DPO na ‘yan sanda da wasu jami’an tsaron bakwai a garin Nasko dake cikin jihar Nejan.

Rahotanni dai sun nuna cewa maharan sun auka ne a garin Bangi hedikwatar karamar hukumar Mariga inda suka nufi ofishin ‘yan sanda to amma sai gamayyar jami’an tsaron suka yi kansu al’amarin da yasa aka tafka gumurzun da yayi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindiga sama da 100 da kasowa yanzu ba’a tantance yawan suba tare kwace baburansu sama da 50, sannan a cikin wannan fafatawa ne aka ce wani ‘dan sanda guda ya rasa ransa.

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Nejan akan wannan sabon hari, to amma gwamnatin Jihar ta tabbatar da kai wannan sabon hari.

Karamar hukumar ta Mariga dai mai iyaka da jihohin Zamfara da Kaduna da kuma jihar Kebbi ta dade tana shan bakar wahalar wadannan ‘yan bindiga inda rahotanni suka nuna cewa a yanzu haka akwai garuruwa sama da 300 da suka zama kangaye saboda al’ummomin dake cikinsu sun tsere domin neman tsira da rayukansu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Jami’an Tsaron Najeriya Sun Tarwatsa Wasu ‘Yan Bindiga Da Suka Kai Hari Ofishin ‘Yan Sanda A Jihar Neja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

XS
SM
MD
LG