Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Yaki Masu Sace Mutane Yadda Take Yaki da Boko Haram - El-Rufai


Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da ma wasu sun ce dole ne gwamnatin tarayya ta yaki masu haddasa muggan ayyukan kamar yadda take yakar Boko Haram ta kuma kawar da wasu abubuwan dake haifar da wadannan munanan dabi'u.

Idan ana son magance sace sacen mutane da fashi da makami akwai bukatar a baza jami'an tsaro a duk dazuzzukan Kaduna, inji gwamnatin jihar.

Gwamna Nasiru El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta yi iyakar tata kokarin saboda batun satar mutane ba a Kaduna kawai ya tsaya ba. Jihar ta dauki duk matakan taimaka wa jami'an tsaro su shawo kan lamarin a jihar, inji gwamnan.

A cewar gwamna El-Rufai, a gwamnatance an gaya wa gwamnatin tarayya ta baza jami'an tsaro cikin duk dazuzzukan da wadannan bata-garin ke fakewa ciki, a yake su yadda ake yaki da Boko Haram. Gwamnan ya ce dole ne a yi amfani da sojojin kasa da na sama da kuma 'yan sanda a fatattake su.

Wasu sun yi tsokaci akan dalilan dake haddasa sace-sacen mutane da kisan gilla da ake yi a arewa. Barrister El-Rubair Abubakar, lauya mai zaman kansa a jihar Kaduna, yana ganin akwai dalilai da yawa da suke haddasa muggan halayen. A cewarsa dalili mafi karfi shi ne yadda satar mutane ta zama hanya mafi sauki ta samun makudan kudade. Abu na biyu gwamnati ta kasa daukan matakai kwarara akan waddanda suke garkuwa da mutane. Inji Barrister Abubakar da gwamnati tana yi musu hukumci mai tsanani da an rage yi ko kuma an daina.

Bugu da kari, Barrister Abubakar ya gano wata matsala babba a tsarin tsaron Najeriya inda sau tari idan an kama masu garkuwa da mutane sai a tarar akwai jami'an 'yan sanda da na sojoji a cikinsu. Lamarin yana kara dagula yaki da bata gari.

Akan kashe-kashe kamar abubuwan dake faruwa a jihohin Nasarawa da Binuwai da Kudancin Kaduna, Barrister Abubakar ya ce matsalolin su ne kabilancin addini da kabilancin yare kuma idan ba'a kawar da su ba, to ba za'a samu zaman lafiya da lumana ba a arewa.

Malam Bello Habibu cewa ya yi akwai karancin jami'an tsaro kuma su jami'an na yanzu yawancinsu suna da hannu a cikin abubuwan dake faruwa. Shi ma Yusuf Idris cewa ya yi akwai sakacin gwamnati saboda babu wanda ya fi karfin gwamnati sai dai ta kyaleshi. Injishi an kama yaro ya yi kisa amma daga baya sai a ganshi yana yawo a hanya saboda an sakoshi. Wani kuma cewa ya yi gwamnatin APC ce ta kasa.

Ga Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG