Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Adamawa Ta Fara Tunanin Hana Saka Hijabi A Wasu Yankunan Jahar


Wasu ‘yan mata yan kunar bakin wake suka kai hari a Maiduguri, Nuwamba 26, 2014.

A yayin da ake ganin zaman lafiya ya fara samuwa a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya, inda yawancin masu gudun hijira suka fara koma garuruwansu sai gashi a ‘yan kwanakin nan an samu tashin boma-bamai.

Cikin ‘yan kwanakin nan anyi fama da tashin bama-bamai da ke da nasaba da rikicin Boko Haram, a Jahohin Borno da Adamawa. Tashin bam na baya bayan nan shine wanda ya faru a kasuwar garin Madagali, wanda wasu mata ‘yan kunar bakin wake suka tayar har yayi sanadiyar rayuka. Sai kuma tashin bam da aka samu a karshen makon nan a garin Maiduguri, wanda shima yayi sanadiyar asarar rayuka.

Wannan batu dai ya fara tayar da hankulan al’ummomin da suka fara komawa yankunansu da aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram.

A zantawarsa da Muryar Amurka, gwamnan jahar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya nuna kaduwarsa game da abubuwan da suke faruwa, ya kuma ce bai kamata jama’a suki komawa garuruwansu ba.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin jahar Adamawa ta fara tunanin hana saka hijabi a wasu yankunan jahar, biyo bayan yawaitar samun hare haren kunar bakin wake.

Tun bayan fara rikicin Boko Haram a Najeriya, an sami asarar dubban rayukan mutanen da basu jiba basu gani ba, haka kuma rikicin ya raba Miliyoyin mutane da muhallansu da tilasta musa zama ‘yan gudun hijira.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG