Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuka Sun Salwanta a Zaben Rivers


Wani Jami'in tsaro a Jihar Rivers da ke Najeriya

Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, sun nuna cewa an yi asarar rayuka yayin da ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki na jiha da na tarayya.

Bayanai sun nuna cewa tarzoma ta barke a wasu sassan jahar inda har aka sace akwatunan zabe.

A wasu lokaci kamar yadda bayanai ke nuni, an samu wasu da ke kwace katunan zabe daga hanun masu kada kuri’a a zaben da aka gudanar a jiya Asabar a jahar.

An ruwaito mutuwar mutum guda a karamar hukumar Tia a yankin Luawii da ke jahar, kamar yadda wakilin Muryar Amurka ya tabbatar.

Akwai kuma bayanai da ke nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kaikaici wata mazaba da ke yankin Bodo inda su ka yi ta harbi a sama, daga baya kuma suka kwashe kayayyakin zabe bayan da mutane su ka watse.

Rahotannin sun ce mutum guda ya mutu a wannan wuri.

Sai dai hukumomin tsaron jihar sun ce ba su da rahoton mutuwar mutum ko guda ko kuma tashin hankali a wani wuri.

Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto ya ce wannan al’amari da ya faru, ya dasa alamar tambaya kan irin shirin da jami’an tsaron su ka yi ikrarin sun yi gabanin zaben.

Ya zuwa yanzu bayanai sun yi nuni da cewa a na dakon sakamakon zaben.

Shi dai wannan zabe ana karawa ne tsakanin manyan jam'iyun kasar, wato PDP mai adawa da kuma APC mai mulki, inda kowanensu ke so ya lashe kujerun mazabun jihar.

Saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG